Take a fresh look at your lifestyle.

Yan Sandan Jihar Neja 513 Sun Samu Karin Matsayi

0 367

Sifeta janar din yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya karawa jami’an yan sandan kasar su 31,465 manya da kananan su karin girma a  makon da ya gabata, inda jahar Neja ke da 513 cikin wadanda suka sami karin mukamin.

Bisa tsarin aikin Yan sandan CP Ogundele Ayodeji ya sanyawa wasu daga cikin jami’an Sabon mukamin su ciki har da matakamkin kwamishina mai kula da operation DCP Adamu Isa Ngojin da matakamkin kwamishina ACP mai kula da sashen Mulki Yusuf Yelwa.

A lokacin da yake Sanya masu sabbin mukaman kwamishinan ya bukaci su da su kara himma wajan kawo sauyi a ayyukan su.

CP Ogundele Ayodeji ya Kuma bukaci su da su nuna kwazo a dukkanin ayyukan su domin nunawa sauran misali, inda a karashe ya taya su murnar samun karin girman.

Wasu daga cikin jami’an da suka sami Karin girman a hedikwatan rudunar dake Minna a bangaran manya akwai; Inspector Barnabas Maisamari  sai David Musa da Masud Abubakar da Hauwa Tanko da Grace Stephen da Ismaila Garba sai Ibrahim Musa da Albert Albara da Kuma Shehu Isah.

Inda a bangaran kananan kuma akwai CPL Bathsheba Hassan da Musbau Yusuf da Kuma Adamu Mohammed.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *