Shugaba Bola Tinubu na cikin wata ganawa da gwamnonin jihohi 36 na Najeriya.
Taron wanda aka fara shi da karfe 11:20 agogon GMT, yana gudana ne a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.
Sabon shugaban kungiyar Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ne ya jagoranci gwamnonin a karkashin kungiyar gwamnonin Najeriya.
Wannan dai shi ne karon farko da Shugaban kasar ke ganawa da Gwamnonin baki daya, tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Ana sa ran taron na yau zai tattauna ne kan matsalar tsaro a fadin kasar nan tare da kuma tabo batun kaddamar da majalisar dokokin kasar a mako mai zuwa, yayin da ake ci gaba da tuntubar shugabannin majalisar ta 10 da nada mukamai a sabuwar gwamnatin shugaba Tinubu.
Leave a Reply