Gwamnonin Najeriya (gamayyar kungiyoyin zababbun gwamnonin jihohin kasar nan 36) sun amince da tsarin shiyyar da jam’iyyar APC ta yi na zaben shugabannin majalisun dokokin kasar karo na 10.
Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ne ya sanar da hakan ta wata sanarwa da dan majalisar wakilai Tajudeen Abbas ya rabawa manema labarai a Abuja bayan ya karbi bakuncin tawagar hadin guiwa ta Majalisa ta 10th.
Abiodun ya ce shi da abokan aikinsa sun dauki matakin ne bayan wata tattaunawa da suka yi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a Abuja.
“A yayin ganawar Tinubu ya nemi goyon bayan gwamnoni ga ‘yan takarar APC – domin a saukake musu zabe.
“Yana da hakkin shugaban kasa ya nemi wadanda za su saukaka masa aikinsa. Ya yanke shawarar tare da hadin gwiwar jam’iyyar cewa wadannan su ne mutanen da yake son yin aiki da su.
“Dukkanmu a layin jam’iyya mun shiga cikin abin da Shugaban kasa ya fada mana. Mun yi ganawar tamu bayan mun gana da shi kuma muka yanke shawarar cewa mu marawa shugaban kasa baya,” in ji Abiodun.
Leave a Reply