Take a fresh look at your lifestyle.

APC ta yi Allah-wadai da mamaye gidan tsohon Gwamna Matawalle na jihar Zamfara

0 120

Reshen jam’iyyar APC mai mulki a shiyyar Arewa maso Yamma, ya koka kan yadda ‘yan sanda da jami’an DSS suka mamaye gidajen tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Dakta Bello Matawalle.

 

Jam’iyyar ta bayyana lamarin a matsayin rashin bin doka da oda, inda ta ce, “Wannan yunkuri ne na neman ganin bayan Gwamna da wasu jami’an gwamnati da suka yi wa jihar hidima a shekaru hudu da suka wuce.

 

Da yake jawabi ga manema labarai a sakatariyar shiyyar na ofishin jam’iyyar da ke Kaduna, Sakataren Yada Labarai na shiyyar, Musa Mada ya yi Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin barna.

 

A cewarsa, ayyukan da aka gudanar a gidajen Gusau da Maradun na tsohon Gwamna sun sabawa sashe na 34, 35, 37, 41 da 42 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 kamar yadda aka yi wa kwaskwarima.

 

Mada ya ce; “Binciken da muka yi dangane da mamayar da aka yi a gidajen Matawalle, ya tabbatar da cewa an kai harin ne ba tare da wani sammaci da jami’an ‘yan sanda da na DSS suka gabatar ba kafin su aiwatar da lamarin.

 

 

“A kan wannan batu, muna so mu yi kira ga Sufeto Janar na ‘yan sanda da ma’aikatar tsaron jihar da su gaggauta binciki lamarin tare da gurfanar da su a gaban kotu. Wannan saboda, idan ba a binciki lamarin, ’yan bindiga na iya sanya kakin kakin su kai hari da sunan abokan gaba da sunan irin wadannan ayyuka.

 

 

“A matsayinmu na jam’iyya, ba za mu amince da hakan ba, kuma muna kira ga jam’iyyar PDP a jihar, idan har suna da sabani da wani a jihar, su bi tsarin da ya dace bisa doka kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada.” Yace.

 

 

Don haka Mada, ya yi kira ga ‘yan sanda da DSS da su gudanar da wannan lamari cikin tsanaki domin jin dadin jama’a domin kada a ce yana yi wa jam’iyyar PDP aiki a jihar, kamar yadda ya bukaci masu bin jam’iyyar su kwantar da hankalinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *