Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Jihar Ebonyi Ya Nada Malamar Jami’a A Matsayin SSG

0 92

Gwamnan jihar Ebonyi Francis Nwifuru ya nada wata malama a jami’ar jihar Ebonyi dake Abakaliki, Farfesa Grace Umezurike a matsayin sakatariyar gwamnatin jihar, SSG.

 

 

Har zuwa lokacin da aka nada ta, Farfesa Umezurike ta kasance babban malami a Sashen Falsafa da Addini a EBSU.

 

Ita ce matar tsohon kwamishinan lafiya na jihar, Dr Daniel Umezurike.

 

 

Cikakken bayanin nadin nata wanda ke kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na Nwifuru, Dr Monday Uzor ya zo ne sa’o’i kadan bayan Gwamnan ya rantsar da wasu manyan mataimaka na musamman guda biyu da mataimaka na musamman guda 20 a ranar Juma’a.

 

 

Sanarwar ta ce, “Gwamnan jihar Ebonyi, mai girma Rt. Hon. Francis Ogbonna Nwifuru ya amince da nadin Farfesa Grace Umezurike a matsayin sakatariyar gwamnatin jihar Ebonyi.

 

“Nadin ya fara aiki nan take.

 

“Za a rantsar da ita a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, 2023.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *