Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu GCFR ya rattaba hannu kan kudirin ba da lamuni na dalibai domin ya zama doka, domin cika daya daga cikin alkawuran da ya dauka na ‘yantar da tallafin ilimi a kasar.
Mista Dele Alake, memba a kungiyar dabarun shugaban kasa ne ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar gwamnati a yammacin ranar Litinin a Abuja.
A cewar Alake, wanda ya samu rakiyar sauran ‘yan kungiyar da suka hada da Mista Tunde Rahman da Abdulaziz Abdulaziz da kuma babban sakataren ma’aikatar ilimi David Adejoh, sabuwar dokar cika daya daga cikin alkawurran zabe na shugaba Tinubu. .
Da aka tambaye shi ko sabuwar dokar ba za ta karfafa hauhawar farashin kudin makaranta ba, Alake ya ce dukkan al’amura biyun ba su da alaka, inda ya ce manufar dokar ita ce a taimaka wa dalibai marasa galihu su samu damar samun ilimi a kasar nan.
Ya ce: “Muna matukar farin cikin sanar da ku cewa, ‘yan mintoci kadan da suka wuce, Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan dokar ba da lamuni na dalibai da kuma dokar rancen dalibai, duk kun san abin da ya kunsa, abin da yake nuni da ma’anar.
“Wannan shi ne alkawarin da dan takarar shugaban kasa na wancan lokacin, Bola Ahmed Tinubu ya yi a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa, na cewa zai dawo da batun rancen dalibai a kan gaba, kuma yau alkawarin da ya dauka ya cika.
“Yanzu ya sanya hannu kan wannan kudirin doka, wanda daga yanzu, zai ba wa dalibanmu marasa galihu damar samun lamuni na gwamnatin tarayya don biyan bukatunsu na neman ilimi ko sana’arsu kuma haka ake yi a sauran lokutan da suka ci gaba a duk duniya.”
Leave a Reply