Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Shugabannin Majalisun Dokokin Kasar

0 130

Shugaba Bola Tinubu yana ganawa da sabon shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas.

Mutanen biyu sun dira a fadar shugaban kasa tare da wasu manyan jami’an majalisun dokokin kasar a yammacin ranar Talata, jim kadan bayan kammala zabensu da rantsar da su a majalisar dattawa da ta wakilai.

Akpabio da Abbas, shafaffu ‘yan takara masu lamba uku da hudu ne suka lashe zabensu kamar yadda aka yi hasashe.

Da bullowar su, sabuwar gwamnati a hankali tana kafawa tare da jagorancin rundunonin gwamnati guda uku a yanzu.

Ana sa ran Shugaban Majalisar Dattawa da Shugaban Majalisar Wakilai za su yi jawabi ga ‘yan jaridu a karshen ganawar da suka yi da shugaban Najeriyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *