Lauyar Kare Hakkin Bil’adama Ta Yi Allah Wadai Da Sace Philip Mehrtens Da ‘Yan Tawaye Suka Yi a Papua
Wata Lauya Maryam Musa Sambo, mai fafutukar kare hakkin bil’adama, ta yi Allah-wadai da yin garkuwa da Kyaftin Phillip Mark Mehrtens, da ‘yan tawaye dauke da makamai suka yi a lardin Papua na Indonesiya.
A wata sanarwa da lauyar kare hakkin bil’adama Sambo Ta fitar a Abuja, Najeriya ta ce: “Sace da garkuwa da Kyaftin Phillip Mark Mehrtems, wani matukin jirgin sama na kamfanin Susi Airways na Indonesiya na daya daga cikin hare-haren kungiyar ‘yan aware na baya-bayan nan.
Barista Sambo wacce kuma mamba ce a kungiyar lauyoyin mata ta FIDA ta kasa da kasa, ta bayyana sace Captain Mehrtens a matsayin zalunci, rashin mutuntaka, wulakanci da kuma keta hakkinsa na bil Adama wanda ke kunshe a cikin dokokin kasa da kasa da dama.
Ta roki kungiyar da ta saki matukin jirgin domin mutunta hakkin dan Adam domin ya sake haduwa da iyalansa.
“Don haka ina kira ga kungiyar ‘yan awaren da ke karkashin jagorancin Egianus Kogoya da su gaggauta sakin matukin jirgin daga hannunsu saboda mutunta Mutuncin Dan Adam, Dabi’un Dan Adam da ‘Yancin Dan Adam. Ina kuma da yakinin cewa Najeriya a matsayinta na kasa mai karfin huldar diflomasiyya da Indonesiya za ta ba da goyon baya tare da ba da duk wani taimako da ake bukata a Jamhuriyar Indonesiya don magance wannan matsalar. (Taron Asiya na 1955),” in ji ta.
Idan za a iya tunawa, an sace Phillip Mark Mehrtens na Christchurch, matukin jirgin kamfanin Susi Air na Indonesiya, a hannun mayakan ‘yancin kai daga West Papua Liberation Army, reshen kungiyar Free Papua Movement, wadanda suka afkawa jirginsa mai injin guda jim kadan bayan ya sauka. karamar titin jirgi a Paro a gundumar Nduga mai nisa.
Shugaban gundumar Nduga Namia Gwijangge, ya ce jirgin mai dauke da fasinjoji biyar, an shirya daukar ma’aikatan gine-gine 15 da ke aikin gina cibiyar kiwon lafiya a Paro bayan da kungiyar ‘yan tawayen a karkashin jagorancin Egianus Kogoya suka yi barazanar kashe su.
‘Yan tawayen Sparat a yankin Papua na Indonesiya sun fitar da wani faifan bidiyo a ranar Laraba da ke nuna wani matukin jirgin na New Zealand da suka yi garkuwa da su yana mai cewa hare-haren na baya-bayan nan da sojojin Indonesia suka kai na barazana ga lafiyarsa.
An shigar da lardin Papua cikin Jamhuriyar Indonesia a cikin 1969 bayan Majalisar Dinkin Duniya ta dauki nauyin jefa kuri’a. Tun daga wannan lokacin, an sami raguwar masu tayar da kayar baya a lardin.
Leave a Reply