Al’ummar kasar Mali za su kada kuri’a a ranar Lahadi don amincewa ko kin amincewa da gyare-gyaren kundin tsarin mulkin kasar da zai karfafa ikon shugaban kasa gabanin mika mulki da aka yi alkawarin komawa mulkin dimokradiyya a kasar da ke yammacin Afirka.
Kuri’ar raba gardama ita ce ta farko a jerin zabukan da aka shirya gudanarwa da nufin share fagen gudanar da zaben shugaban kasa a watan Fabrairun shekara ta 2024, wanda shugabannin sojojin Mali suka kuduri aniyar gudanar da shi, sakamakon matsin lamba daga kasashen yankin.
Gwamnatin mulkin sojan dai ta jinkirta gudanar da zaben raba gardama har na tsawon watanni uku saboda matsalolin kayan aiki.
Ana kallon kuri’ar na ranar Lahadi a matsayin wata manuniya ta himma da karfin da gwamnatin mulkin soji ke da shi na shirya zabe a kasar da mayakan ‘yan bindiga suka mamaye yankunan arewaci da tsakiyarta.
Bacin rai game da tabarbarewar tsaro ya haifar da mamayar sojoji biyu a cikin shekarar 2020 da 2021, amma gwamnatin mulkin soja ta kasa dakile ta’addanci ko inganta rayuwa a daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya.
Babu wata tabbatacciyar yarjejeniya da ta fito gabanin zaben na ranar Lahadi.
Leave a Reply