Jamhuriyar Nijar ta karrama wasu ‘yan Najeriya shida da lambar yabo ta kasa sakamakon rawar da suke takawa wajen inganta kyakkyawar alaka a tsakanin kasashen biyu. Wadanda aka karrama sun hada da Gwamnonin Najeriya biyu, hadiman shugaban kasa biyu da ‘yan kasuwa biyu. Hakan ya faru ne a ranar Laraba a ranar ‘yancin kai na jamhuriyar Nijar, wanda ake bikin ranar 3 ga watan Agustan kowace shekara. An kebe ranar ne domin tunawa da ‘yancin kai daga kasar Faransa a shekarar 1960 kuma tun daga shekarar 1975 aka amince da ita a matsayin “ranar dashen itatuwa” yayin da ake dasa bishiyoyi a fadin kasar don taimakawa yaki da kwararowar hamada. Da yake bayar da kyaututtukan, shugaba Mohammed Bazoum ya ce kasarsa na mutunta Najeriya a matsayin daya daga cikin makusanta da kawayenta. Wadanda aka karrama sun hada da Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa da takwaransa na jihar Zamfara, Mohammed Bello Matawalle. Sauran sun hada da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa, Sarki Abba, da kuma babban jami’in hulda da jama’a na jihar, Ambasada Lawal Kazaure. ‘Yan kasuwan da suka samu karramawar sun hada da Alhaji Aliko Dangote, shugaban rukunin Dangote da Abdulsamad Rabi’u shugaban kungiyar BUA, kuma an ba su lambar yabo ta “Order of Merit of Niger, Great Master of National Awards”. Shugaba Bazoum ya yaba da kokarin ‘yan Najeriya da suka samu gagarumin ci gaba wajen kara fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu da kuma matsayinsu na wakilan ci gaban zamantakewa da tattalin arziki.
Leave a Reply