Kungiyar Civil Society Action Coalition on Education for All, CSACEFA ta bayyana rashin jin dadin yadda aka rufe makarantun hadin kai a fadin kasar. Shugaban kungiyar CSACEFA na kasa, Mista Sale Abdullahi ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa Muryar Najeriya, a Abuja. Abdullahi ya ce yaran Najeriya sun ga wani mummunan yanayi a lokacin zafafa hare-haren da ake kai wa wuraren karatu a fadin kasar sakamakon ayyukan ‘yan bindiga. “Makonni da suka gabata sun shaida yadda aka rufe makarantu a fadin kasar, na sakandare da manyan makarantu” Ya kara da cewa, “Tun bayan faruwar lamarin Chibok a shekarar 2014, inda aka sace dalibai sama da 276 a yankin Arewa maso Gabas, rikicin ya bazu zuwa yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya ta hanyar kai hare-hare marasa adadi.” Abdullahi ya ce ‘yan fashin na neman a biya su makudan kudade, a wasu lokutan kuma suna kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba, wadanda ya kamata su kasance a hannun waliyyansu ko iyayensu tare da yin alkawarin ganin an sako su ba tare da wani tasiri ba. “A cewar Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ya zuwa yau, an rufe makarantu sama da 11,536 tare da sace dalibai sama da 1,500. Wannan abin zargi ne da kuma tauye hakkin yaran Najeriya na neman ilimi”. Ya nuna damuwarsa cewa rikicin ilmantarwa zai yi tasiri ga cimma burin ci gaba mai dorewa (SDGs) biyo bayan raguwar yawan rajista da riko. Abdullahi ya kuma bukaci gwamnati da ta tuna da kwangilar zamantakewar da ta kulla da iyaye da daliban Najeriya a matsayin babban jigo na yakin neman zabe.
Leave a Reply