Shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya karbi bakuncin shugabannin kasashen Netherlands, da Denmark, wadanda ke Afirka ta Kudu a wata ziyarar aiki ta hadin gwiwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Afirka ta kudu SABC cewa, ziyarar ta firaministan kasar Mark Rutte da takwarar sa na kasar Denmark Mette Frederiksen na da nufin karfafa alakar kasashen uku a fannonin koren hydrogen, da makamashin da ake sabuntawa da kuma samar da makamashi mai inganci.
Kasashen Afirka ta Kudu da Netherlands za su rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa kan koren hydrogen.
Shugabannin Turai sun zo da manyan tawagogin kasuwanci.
Taron Kasuwanci a ƙarƙashin taken “Green Energy Transition and Green Hydrogen Partnerships for Impact” zai mayar da hankali kan muhimman wurare a cikin makamashin kore da hydrogen.
Kasashen Turai na son karya dogaron da suke yi kan makamashin kasar Rasha, kasashen Turai sun yi ta sa ido ga takwarorinsu na Afirka domin cike gibin.
Leave a Reply