Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Kano Ya Umarci Kwamishinonin Da Ya Bada Sunayen Su Ga Majalisa Su Bayyana Kadarori

0 193

Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya umurci dukkanin kwamishinoni 19 da aka Zaba da su bi ka’idojin da’a, tare da bayyana kadarorin su.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran sa, Bature Dawakin Tofa ya fitar a Kano.

 

A cewarsa, ana sa ran wadanda aka zaba za su bayyana kadarorin su kafin majalisar ta tantance su.

 

Gwamnan, a cikin sanarwar, ya sha alwashin cewa babu wani kwamishina da za a rantsar da shi a matsayin mamban majalisar ministoci ba tare da cike fom din bayyana kadarorin da hukumar da’ar ma’aikata ta fitar ba.

 

“Duk sauran masu rike da mukaman siyasa a karkashin wannan gwamnati su ma za su bi umarnin yadda ya kamata,” in ji sanarwar.

 

Gwamna Yusuf ya nanata alkawarin da ya yi wa jama’a cewa gaskiya da rikon amana shi ne tushen tsarin mulkinsa.

 

Ya ce za’a yi amfani da wannan ne ga zakaran shugabanci nagari kamar yadda yayi alkawari a lokacin yakin neman zabe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *