Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Abuja da ake kira da FCT Emergency Management Agency ko kuma FEMA atakaice ta cika shekaru goma cif da kafuwa.
Shugaban hukumar Dr Abbas Idris ya ce a shekaru goma da hukumar ta kwashe da kafuwa ta sami nasararori da dama wadanda suka hada da bayar da dama ga ma’aikatansu zuwa wasu jami’oin kasar nan domin karo ilimi wadda yanzu haka hukumar nada zakakuran ma’aikatan da zasu iya bayar da horo ga ma’aikatan jinkai dake sawu cibiyoyi, sai kuma wayar da kan mazauna birnin Abuja kan matakan kaucewa fadawa bala’oi musamman a lokacin damina, kana sun sami lambobin yabo mabanbanta dangane da yadda suke gudanar da ayyukansu wadda a cewarsa tuni hukumar ta FEMA ta yi wa takwarorinta dake jihohohin Najeriya talatin da shida fintinkau in banda jihar legas dake kudu maso yammacin kasar da suke gogayya da juna.
“kasancewar hukumar sabuwa fil a sanda ya fara jan ragamar ta a shekarar dubu biyu da goma sha uku da aka assasata ya taras da tarin matsaloli da suka hada rashin cikakkiyar dokar gudanar da ayyukanta, amma duk da haka akwai nasarori a zahirance da yan kasa zasu sheda hukumar ta samu cikin wadannan shekaru ciki kuwa har da kai daukin gaggawa a lokacin da aka rika samun tashin bamai –bamai a wasu unguwannin Abuja da suka hadar da tashar motocin haya dake Unguwar Nyanyan da kuma wanda ya tashi a Emap plaza a wuse 2 da kuma wanda aka samu a kuje da dai sauransu” In ji Dr. Abbas
Kazalika, FEMA tace za ta ci gaba da aiki tukuru domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu a kokarinta na sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na ilmantar da jama’a kan matakan kaucewa fadawa bala’oi a birnin na Abuja.
Buguda da kari, Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Abuja ya kara da cewa tarin nasarorin da suka samu ya samu ne sakamakon hadin kai da suke samu daga mazauna birnin Abuja, da hukumomin da nauyin ya rataya a wuyansu dama uwa uba jami’an tsaro da manema labarai dake isar da sakonsu ga al’umma.
A gefe guda kuma ya shawarci ma’aikatansa da su kasance cikin shirin kota kawana kamar yadda suka saba domin ko da yaushe bukatar nemansu ka iya tasowa domin kai dauki a birnin Abuja kamar yadda dokokin gudanar da aikinsu suka tanadar.
Ak
Leave a Reply