Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta cafke wani mutum mai shekaru casa’in bisa zargin mallakar kilogiram 5.1 na tabar wiwi a jihar Sokoto. Kwamandan hukumar na jihar, Mista Adamu Iro ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Sokoto. A cewar Mista Iro, wanda ake zargin wani sojan Najeriya ne mai ritaya, wanda jami’an tsaida da bincike na hukumar suka kama shi a kan tsohuwar hanyar kasuwa a cikin babban birnin jihar. Ya bayyana cewa wanda ake zargin mazaunin kauyen Mailalle ne da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar. “Daga binciken mu na farko, mun lura cewa wanda ake zargin ya shahara wajen kai wa ‘yan fashi da kwayoyi. “Gabashin Sokoto inda Sabon Birni yake ya kasance babbar maboyar ‘yan bindiga. “Saboda haka, mun yi imanin yawancin abokan cinikinsa ‘yan fashi ne wadanda suka dade suna ta’addanci a yankin,” in ji Iro. Mista Adamu Iro ya bayyana cewa rundunar za ta gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike. Sai dai ya bukaci hadin kai da fahimtar jama’a wajen baiwa rundunar bayanan tsaro da suka dace da za su taimaka wajen kawar da jihar daga matsalolin tsaro. Kwamandan jihar ya yabawa duk masu ruwa da tsaki a harkar tsaro bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen baiwa NDLEA tallafin da ake bukata domin ganin jihar Sokoto ta kubuta daga duk wani nau’in safarar miyagun kwayoyi.
Leave a Reply