Shugaba Bola Ahmed Tinubu GCFR zai ziyarci jihar Ogun a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuni, 2023.
Shugaban na Najeriya zai ziyarci Sarakunan jihar, Alake na Egbaland, Oba Adedotun Gbadebo, a Abeokuta, babban birnin jihar da kuma Awujale da Paramount Sarkin Ijebuland, Oba Sikiru Adetona a Ijebu-Ode.
Wani mai taimaka wa Gwamna Dapo Abiodun, Babatunde Olaotan, ne ya bayyana hakan a cikin sakon gayyata da ya aikewa shugabannin jam’iyyar APC da magoya bayansa, ranar Laraba.
“Gwamna Dapo Abiodun – CON na gayyace ku da ku don ku maraba da Mai Girma, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu – GCFR wanda zai kawo mana ziyara gobe, 29 ga Yuni, 2023 a Ijebu-Ode da Abeokuta.
“Dukkan shugabannin jam’iyyarmu, dattawa da magoya bayanmu na Gundumar Sanata ta Ogun ta Gabas su hallara a wurin Awujale da karfe 8:30 na safe yayin da shugabannin jam’iyyarmu, dattawa, mambobinmu da magoya bayanmu na Ogun ta Tsakiya da Ogun ta Yamma su hallara a wurin Alake da karfe 10:30 na safe.”
Idan dai za a iya tunawa, ziyarar ta karshe da Shugaba Tinubu ya kai jihar ita ce ranar 25 ga watan Janairun 2023, lokacin da jirgin yakin neman zabensa na shugaban kasa ya mamaye Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Leave a Reply