Take a fresh look at your lifestyle.

NAJERIYA TA BAI WA KANFANONIN SARRAFA MAGUNGUNA BILIYON N100

194

Gwamnatin Najeriya ta bada bashin Naira Biliyon N100 ga kanfanonin sarrafa Magununa da masu saka jarin bangaren kiwon lafiya.

Wannan bashin dai zai taimaka wajen bunkasa sarrafa magunguna da kayayyakin kiwon lafiya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da haka ranar Talata a Abuja,lokacin day a karbi bakuncin Mambobin kungiyar Kiwon lafiya ta Najeriya, NMA.

Shugaban yayi bayani cewa wannan bashin zasu samu ne daa hannun babban bankin tarayya CBN domin karfafa wa kanfanonin Magunguna masu zaman klansu.

Yace kwamitin lafiya da mataimakin Shuaban kasa Yemi Osinbajo, ya jagoranta na duba yiwuwar samar da hanyoyin da suka dace na karfafawa da garambawul din banaren kiwon lafiyar kasa,domin inganta wannan banare ta yadda al’uma zasu anfana cikin sauki.

Dangane da yawan kwararrun dake fita kasashen waje neman aiki kuwa,Shugaba Buhari yace ya umurci Ministan lafiya day a duba lamarin ta yadda zaa juyar da ficewa kasar waje da anfani da kwakwalwa ga kwararrun maaikatan lafiya ‘yan Najeriya daga kasar waje yin anfani da fasahar su zuwa gida Najeriya.

Yayi kira ga masu ruwa da tsaki na kungiyar lafiya das u mara wa kudurin Gwamnati baya wajen aiki da manufar kwamitin na bangaren kiwon lafiya domin anfanin ‘yan Najeriya a karni na 21.

Shugaban ya jinjina wa Kungiyar,wadda itace lema ga sauran bangarorin maiaakatan lafoiya ta Najeriya,da ta dauki wannan kyakyawan matakai cikin rowan sanyi akan abunda ya shafi tsarin lafiyar a’umar Najeriya.

‘‘Ina mai jinjina wa kwararun maaikatan lafiya da suka bada gudummowar su wajen udanar da aiki lokacin da cutar COVID-19 ta bazama, da shawo kan cutar zazzabin cizon sauro, Kanjamau HIV da tarin fuka, da sauran nasarorin da Likitocin Najeriya mazauna kasashen waje suka cimma. 

‘‘Hanyoyin da muka bi akan annobar COVID-19 ya samu yabo daga kasashen duniya kuma mambobin ku sun taka rawar anai a wannan nasarar.

‘‘Na tuna a shekara ta 2021, Jagororin kungiyar ku masu barin gado NMA sun kawo mani ziyara kuma suka mika bukatun sun a bangaren lafiya, da suka hada da, garambawul ga dokar tsarin kiwon lafiya na kasa NHIS Act; kara inganta kayayakin kiwon lafiya zuwa na zamani a cibiyoyin su; Basuka domin tallafa wa kayayyakin Asibitoci da kuma kafa doki akan likitocin Hakori da bukatar Karin tallafi ga sabbin Jamio’I hudu (4) na kimiyar kiwon Lafiya.

‘‘Ina mai farin cikin sheida muku cewa tuni aka amsa akasarin bukatun da aka gabatar,kana ana nazari akan abun day a shafi shugabanci da dokokin da suka shafe su,’’ inji shi.

LADAN NASIDI

Comments are closed.