Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi kira ga ‘yan siyasar Najeriya da su zama masu maida hankali da zurfin tunani wajen kishin kasa.
Shugaba Buhari yace; “Mu ‘yan Najeriya ne da girman Allah zamu ci gaba da kasancewa ‘yan Najeriya kuma tsintsiya madaurinki daya.’’
Shugaba Buhari ya sanar da haka ne lokacin day a karbi bakuncin tsohon karamin Shugaban tsohuwar Jamiyyar Congress for Progressive Change (CPC) ranar Talata a fadar Shugaban kasa Abuja.
Shugaban yace rashin da’ar da aka nuna da yayi sanadiyar mutuwar miliyoyin mutane daga shekara ta 1967-1970 ba kamata ya maimaita kanshi ba, yayi nuni da kafuwar Jamiyyar CPC a turbar kishin kasa bin doka da hadin kan kasa.
Yace; “Babban burin mu shine Janhuriyar Tarayyar Najeriya. Mu dai ‘yan Adam ne. Muna da namu raunin,amma ina mai tabbatar muku da cewa muna da kishin kasa a zukatan mu.. Mun shiga rigin-gimu daga ranar 15th ga watan Janairu 1966 zuwa yau. Kun san abunda nake nufi da hakan,mun kasha miliyoyin mu domin kasancewa tare.
“Mu ‘yan Najeriya ne kuma zamuci gaba da kasancewa ‘yan Najeriya kuma Najeriya zata ci gaba da zama kasa daya.”
LADAN NASIDI
Leave a Reply