‘Yan sanda a Kenya sun harba barkonon tsohuwa don tarwatsa masu rajin kare hakkin bil’adama da ke kira da a saki mutane da dama da aka tsare a zanga-zangar adawa da gwamnati ranar Juma’a.
Hotunan bidiyo sun nuna gajimare na hayaki mai sa hawaye a babban ofishin ‘yan sanda na Nairobi.
Daga cikin masu zanga-zangar na yau akwai tsohon alkalin alkalai, Willy Mutunga.
Jagoran ‘yan adawa Raila Odinga ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar ranar Juma’a don nuna adawa da karin harajin man fetur da kuma tsadar rayuwa.
Akalla mutum daya ne aka ruwaito ya mutu lokacin da ‘yan sanda suka mayar da martani kan zanga-zangar da aka yi a Nairobi, Mombasa da Kisumu.
Akalla mutane 28 aka kama.
BBC/L.N
Leave a Reply