Take a fresh look at your lifestyle.

PDP A Jihar Katsina Ta Nada Kwamitin Riko

Kamilu Lawal,Katsina,

0 139

Jam’iyyar PDP ta nada kwamitin riko na jam’iyyar reshen jihar Katsina.

 

Wannan nadin na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Mista Debo Ologunagba, ya fitar ranar Juma’a, kuma ya bayyanawa manema labarai a Abuja.

 

Ologunagba ya ce kwamitin zai gudanar da harkokin jam’iyyar a jihar na tsawon watanni uku.

 

Ya ce shawarar da kwamitin ayyuka na jam’iyyar ta kasa ya yi, yin amfani da karfin ikonta ne a karkashin kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP (kamar yadda aka gyara a shekarar 2017).

 

“Kwamitin riko na Katsina zai tafiyar da al’amuran jam’iyyar a jihar na tsawon kwanaki 90 wanda zai fara daga ranar 23 ga watan Yuni,” in ji Ologunagba.

 

Ya bukaci daukacin shugabanni, masu ruwa da tsaki da kuma ‘yan jam’iyyar a Katsina da su kasance da hadin kai da mayar da hankali yayin da suke aiki tare domin karfafa PDP a jihar.

 

L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *