Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima Sen. Kashim Shettima a ranar Asabar ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dan uwansa, Muktar Alkali a Maiduguri, Jihar Borno.
Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu rakiyar iyalan marigayi Alkali tare da Gwamna Babagana Zulum na Borno da wasu manyan jami’an gwamnati, ya yaba da irin halin kirki na marigayin a matsayin gogaggen mai kula da al’umma.
Daga baya mataimakin shugaban kasa da Gwamna Zulum suka shiga yi wa iyalan marigayi Alkali addu’a.
Marigayin dai tsohon Provost ne, na kwalejin aikin gona ta jihar Borno dake Maiduguri.
Ya kasance mai bayar da shawarar samar da aikin yi ga matasa a matsayin hanyar magance kalubalen talauci da rashin tsaro a kasar.
Taron ya samu halartar manyan ‘yan Najeriya da malaman addinin Musulunci da sarakunan gargajiya da suka hada da Shehun Bama, Umar Shehu Kyari.
Marigayin ya rasu ne a ranar Juma’a 7 ga Yuli, 2023 yana da shekaru 57, ya bar mata da ‘ya’ya.
Leave a Reply