Take a fresh look at your lifestyle.

SHUGABA BUHARI YA NADA LAWAL MATAIMAKIYA TA MUSAMMAN

0 239

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya nada tsohuwar sakatariyar din-din-din, Ofishin Kula da ayyukan bunkasa muhalli (EPO), Habiba Muda Lawal, a mukamin mai bada shawara ta musammn ga Shugabn kasa akan manufofi da shirye shirye.

Kafin nadin nata, Dr Lawal ta yi nasarar sanya ido akan tawagar da ta tabbatar da gudanar da shugabanci,Ganewa,tsare-tsare da aiwatar da aiyuka da suka shafi aiyukan kula da kalubalen muhalli a fadin kasar.

Tayi karatu a Jamiar Ahmadu Bello dake Zaria daga shekara ta 1982 zuwa 1986 tana da digiri na farko akan Kimiya,daga nan ta samu lambar yabo ta dalibar da tayi fice daga kanfanin sarrafa Taba daga shekara ta 1984/1985, Lambar yabo ta dalibar da tafi daliba rubutun kamala aikin Digiri a shekara ta 1985/1986.

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *