Gwamnatin Mali ta sanar da kisan sojoji 42 a wani harin ‘yan taadda ranar Lahadi Karin mutuwar da aka samu daga 17.
Rahotanni na cewa akalla sojoji 22 suka jikata, kana aka kashe ‘yan taadda 37 .
An kai harin ne a garin Tessit, yankin da ake kai hare-hare dake kan iyakar Mali da kasashen, Burkina Faso da Nijar.
KARANTA: Militant Kills 17 Soldiers in Mali
Wannan harin shine mafi muni ga kasar Mali a cikin shekaru 10 da ‘yan bindigar masu rajin kafa Islama suka gudanar.
Dubun dubatar mutane suka kaura daga yankunan, akkalla miliyoyin mutane ne ke gudun hijira a yankin Sahel.
LADAN NASIDI
Leave a Reply