Take a fresh look at your lifestyle.

MINISTA YA BUKACI MATASAN NAJERIYA SU BADA GUDUMMOWAR GINA KASA

0 181

A bukin ranar matasan duniya,Ministan Matasa da ci gaban wasanni na Najeriya ,Sunday Dare yayi kira ga matasan Najeriya su zama masu bada gudmmowar gina kasa da kaucewa duk wata mumunar hanyar.

Ya sanar da haka ne a jawabin Ministan da Daraktan hulda da Manema labarai, Mohammed Manga ta shafin Tweeter ranar Juma’a , 12 ga watan Agusta 2022.

Ministan ya jaddada kudurin gwamnatin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhar na samar da kyakyawan yanayin ci gaban Matasa,ya bukace su das u kasance masu anfani da wannan damar domin gogayya da sauran duniya.

Ya kamata mu kuma yi anfani da wannan dammar da Gwamnati ta samar wajen horaswa da tallafawa matasa ta yadda zasuyi aiki kafada da kafada da na sauran duniya domin cimma yunkurin mu na ci gaban Najeriya.”

Ana bukin ranar matasan duniya a kowace shekara a ranar 12 ga watan Agusta domin janyo hankalin matasa na bada goyon baya gad a matasa ke bayarwa a duniya.

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *