Take a fresh look at your lifestyle.

NAJERIYA TA BULLO DA TSARIN KIWON LAFIYAR ‘YAN GUDUN HIJIRA

0 173

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira, da wadanda suka rasa matsuguni da balao’I a Najeriya ta kaddamar da shirin kiwon lafiyar ‘yan gudun Hijira, IDPS.

Hakan na cikin kudurin Hukumar na tabbatar da an bada kula na musamman ga ‘yan gudun hijira.

Kwamishiniyar Tarayya, Imaan Suleiman-Ibrahim ta kaddamar da gwajin farko a sansanin ‘yan gudun hijira dake Waru IDP, wani yanki dake cikin babban birnin tarayya, Abuja.

Ta kara da cewa,akalla mutane 270 zasu ci gajiyar shirin.

Ina mai mayukar farin ciki game da wannan kudurin kiwon lafiya da zai taimaka kyauta ga sansanin ‘yan gudun hijira IDPs, Wadanda suka dawo da wadanda ke cikin hadarin neman mafaka.

Tace duk wadannan kudurin zai shafi duk abunda ya danganci bukatu na kiwon lafiyar dan Adam.

 

Daya daga cikin wadanda sukaci gabjiyar shirin a Waru , Chiwendu Peter tace taji dadi da ta kasance daya daga cikin wadanda sukaci moriyar wannan tallafi.

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *