Shugaban Najeriya , Muhammadu Buhari ya nada tsohon mataimaki akan bangaren sada zumunta na zamani, Bashir Ahmad,a mukamin mataimaki na musamman akan Naurar zamani mai yatsu.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya tabbatar da wannan nadin a cikin wasikar aiki dad a aka baiwa Ahmad, ranar 20 ga watan Yuli, 2022.
Mustapha yace wannan mukamin zai fara aiki daga ranar 19 ga watan Yuli 19, 2022.
Bashir Ahmad ta nuna godiyar shi ga Shugaban kasa saboda wannan mukamin a shafin Twitter din shi
This is an honor. Thank you Baba @MBuhari, President of the Federal Republic of Nigeria for finding me worthy again and again, this time as your Special Assistant on Digital Communications. I will continue being a good ambassador of your administration, Baba. ‘Alhamdulillah’! https://t.co/9pNKmsWihN
— Bashir Ahmad (@BashirAhmaad) August 14, 2022
A baya dai Bashir ya ajiye aiki na mukamin matsayin mataimakin shugaban kasa akan Naurar Zamani sakamakon umurnin da Shugaban kasa ya baiwa duk mai shaawar ysayawa Takara a zabuka ya ajiye mukamin shi.
Mataimakin ya tsaya takarar Sanata mai wakiltar Gaya,Ajingi da Albasu karkashin tutar jamiyyar All Progressives Congress (APC) a majalisar kasa.
Wannan mayaimakin shugaban kasa akan harkokin sadarwar zamani ne kadai fadar Shugaban kasa ta amince ya dawo bakin aiki.
Sauran ministoci da mataimakan Shugaban kasa da suka fadi a zaben fidda gwani, Ahmad kadai ne ya dawo bakin aiki.
LADAN NASIDI
Leave a Reply