Take a fresh look at your lifestyle.

SHUGABAN ‘YAN SANDAN NAJERIYA YA BADA UMURNIN KARA TSARO A MAKARANTU

113

Shugaban ‘yan sandan Najerioya (IGP) Usman Alkali Baba,ya bada umurnin karin Jami’an tsaro a Makarantu,Asibiti da dukiyoyi a fadin kasar.

Jami’in hulda da Jama’a na rundunar ‘yan sanda, Olumuyiwa Adejobi, ya sanar da haka a shafin sada zumunta na Twitter ranar Lahadi 14 ga watan Agusta, 2022.

Shugaban rundunar ‘yan sandan ya bada wannan umurni ne sakamakon rahotanni harkokin tsaro a fadin kasar.

“Hakazalika IGP ya kuma baiwa ‘yan sandan sintiri su rinka bincike da kame domin dakile  duk wata hanyar aikata manyan laifuka a jihohi da Birane a duk faadin kasar.”

Yayi kira ga Jami’an tsaron su rinka tara bayanan sirri da kuma kama duk  wanda ya aikata laifi ba bias doka da oda bad a kuma zakulo duk maboyar masu laifi.

 

LADAN NASIDI

 

Comments are closed.