Take a fresh look at your lifestyle.

MINISTAN ILIMI YA GANA DA JAMI’A

Daga Temitope Mustapha, Abuja

106

Ministan Ilimi, Adamu Adamu,  yana ganawa da shugabannin kungiyar malaman jami’o’i, ASUU domin warware yajin aikin watanni 6 da aka kwashe ana yi a jami’o’in gwamnati.

Taron dai na zuwa ne bisa umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na magance muhimman bukatun kungiyar da suka hada da amincewa da tsarin bayyanin gaskiya a jami’o’in (UTAS) ba wai kawai albashin malaman da ke yajin aiki ba da aka dakatar tun watan Maris din 2022.

Ana sa ran taron zai kawo karshen yajin aikin da ya addabi jami’o’in gwamnati da kuma mayar da jami’o’i a fadin kasar.

A ranar Alhamis din makon nan ne ake sa ran Ministan zai yi wa Majalisar Zartarwa ta Tarayya bayani.

 

 

Aisha Yahaya

 

 

Comments are closed.