Take a fresh look at your lifestyle.

Za a ci gaba da rufe sararin samaniyar Sudan har zuwa ranar 31 ga Yuli

0 94

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sudan ta kara wa’adin rufe sararin samaniyar kasar Sudan har zuwa ranar 31 ga watan Yuli, in ban da agajin jin kai da na jigilar jama’a tare da izini daga hukumomi, in ji filin tashi da saukar jiragen sama na Khartoum a ranar Litinin din nan.

 

Wannan keɓancewar na nufin tabbatar da cewa kayan masarufi sun isa ga mabukata da kuma saukaka korar mutanen da rikicin ya shafa.

 

An rufe sararin samaniyar Sudan don zirga-zirga akai-akai bayan da rikicin soji ya barke tsakanin sojojin kasar da dakarun Rapid Support Forces (RSF) a tsakiyar watan Afrilu.

 

Afirkanews/L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *