Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya sanar da cewa, za a gudanar da taron BRICS na wata mai zuwa da ake bukatar mutum ya o da kan shi.
Afirka ta Kudu ita ce shugabar BRICS a halin yanzu, kungiyar kasashe da suka hada da Brazil, Rasha, Indiya da China wadanda manufarsu ita ce kalubalantar mamayar Amurka da Turai a duniya.
An gayyaci shugaban kasar Rasha Vladmir Putin zuwa halartar taron duk da cewa kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ke nema ruwa a jallo kan zargin da ake yi wa Rashan na korar yaran Ukraine ba bisa ka’ida ba.
“Za mu yi taron koli na BRICS na zahiri, kuma dukkanmu mun kuduri aniyar yin taron koli inda za mu iya kallon ido da juna. Ba mu daɗe da gudanar da taron koli na zahiri ba, kusan shekaru uku yanzu. Don haka, ku yi hakuri in ba ku kunya, ba zai zama mai kama da gaskiya ba, ”in ji shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa.
Afirka ta Kudu ba ta yi Allah-wadai da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ba, tana mai cewa ba ta nuna son kai ba, kuma ta fi son tattaunawa, wanda take ingizawa.
A watan da ya gabata, Ramaphosa ya jagoranci tawagar wanzar da zaman lafiya na kasashen Afirka bakwai da suka hada da wakilai daga Jamhuriyar Congo, Masar, Senegal da Uganda, a wani yunƙuri mai cike da tarihi na samar da zaman lafiya tsakanin Kyiv da Moscow.
Africanews/L.N.
Leave a Reply