Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Abuja, babban birnin Najeriya bayan halartar taron kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) karo na 63 a Guinea Bissau.
Shugaban wanda ya sauka a yammacin jiya Litinin, ya samu tarba a reshen shugaban kasa na filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Abuja tare da shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, tsohon gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu, tsohon gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi. Ganduje
A yayin taron an zabi shugaban Najeriyar a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS.
A jawabinsa na karbar, shugaba Tinubu ya yi alkawarin yin aiki domin cimma manufofin kungiyar yankin.
Ya kuma umarci takwarorinsa da su hada kai domin yaki da juyin mulkin da ya sake kunno kai a yammacin Afirka.
Leave a Reply