Majalisar Wakilai ta bukaci Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa NUC, da ta gaggauta dakatar da aiwatar da karin kudaden da Jami’o’in Tarayya ke yi a fadin Najeriya.
Hakan ya biyo bayan kudirin da wani dan majalisa daga jihar Kano, Mista Aliyu Madaki, ya gabatar yayin zaman majalisar a ranar Talata.
Dan majalisar ya bayyana damuwarsa kan yadda karin kudaden da wasu jami’o’in gwamnatin tarayya ke yi a fadin kasar nan na faruwa ne sabanin yadda talauci ke kara ta’azzara, hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi da kuma hauhawar farashin man fetur a baya-bayan nan.
Mista Madaki ya lura cewa karin da aka yi zai iya haifar da cikas ga dimbin daliban da ba za su iya biyan kudaden ba, yana mai cewa yayin da da yawa daga cikinsu za a tilasta musu jinkirta karatunsu, wasu na iya daina karatu.
A cewarsa, “harin na iya kara ta’azzara halin da kasar nan ke ciki, ganin cewa tuni dalibai suka fara yin barazana da ka iya haifar da tada kayar baya ga gwamnatin tarayya, wanda zai haifar da mummunar illa ga kasa baki daya.
“Haka kuma ana fargabar cewa karuwar yawan barin jami’o’i na iya kara ta’azzara rashin tsaro a Najeriya domin daliban da ke cike da takaici na iya gano inda ba su dace ba don bayyana kokensu.”
Ya kara da cewa ilimin manyan makarantu ya zama wajibi wajen bunkasa ci gaba, rage radadin talauci, da bunkasa ci gaban kowace kasa.
Majalisar ta kuma umurci kwamitin kula da manyan makarantu da ayyuka (a lokacin da aka kafa shi) ya binciki lamarin, da nufin samar da dawwamammen mafita kan kalubalen da ake fuskanta a bangaren ilimi.
Leave a Reply