Take a fresh look at your lifestyle.

Hajj 2023: Jihar Kwara Ta Dawo Da Alhazai 1,600, Mutum Daya Ya Rasu

0 130

Alhazai dubu daya da dari shida (1,600) ne daga jihar Kwara dake arewa ta tsakiya Najeriya da suka gudanar da aikin hajjin bana zuwa kasar Saudiyya ta hukumar jin dadin alhazai ta jihar kawo yanzu an dawo da su gida.

Sakataren zartarwa na hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ya shaidawa Muryar Najeriya a wata hira da ya yi da cewa, tuni aka fara gudanar da jirage shida da na baya-bayan nan ta jirgin Air Peace dauke da alhazai 271 da suka isa a yau Lahadi.

Suna cikin daukacin mutane 3,546 da hukumar ta dauko daga jihar domin gudanar da aikin hajjin bana zuwa kasa mai tsarki.

Sakataren zartarwa ya yi kira ga sauran alhazan da har yanzu ba a dawo da su gida ba domin su yi hakuri domin jihar Kwara za ta ci gaba da wani jirgin a ranar 19 ga watan Yuli yayin da ake fatan za a kammala jigilar jirgin na karshe kafin karshen wannan watan.

A cewarsa, jirgin Air Peace da ke aiki a jihar Kwara an mayar da shi jihohin Ondo da Ekiti don jigilar alhazai daga shiyyar.

Mahajjacin Kwara daya ya rasu a kasar Saudiyya

A halin da ake ciki, Abdulsalam ya ce babu wani lamari da aka kama ko tambayoyi daga mahajjatan jihar amma ya tabbatar da cewa wani dattijo mai shekaru saba’in dan asalin Ilorin mai suna Busari Alao ya rasu a kasa mai tsarki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *