A halin yanzu mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abubakar Kyari, yana jagorantar taron gaggawa na kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta kasa, NWC.
An fara taron ne da misalin karfe 10:30 na safe a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da ke Abuja.
Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga jam’iyyar dangane da murabus din shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, rashin halartar taron NWC da ya saba shugabanta ya fito fili.
Muryar Najeriya ta ruwaito cewa Motar Mataimakin Shugaban Kasa ta Arewa na ajiye a bakin Shugaban kasa.
Akwai kuma rahoton murabus din sakataren kasa, Iyiola Omisore bayan murabus din shugaban.
Sai dai Sakataren na kasa yana nan a hedikwatar jam’iyyar APC amma ba ya cikin NWC.
L.N
Leave a Reply