Take a fresh look at your lifestyle.

Makarantu sun rufe kan zanga-zangar tsadar rayuwa a Kenya

0 161

An rufe makarantu a Nairobi babban birnin kasar Kenya da kuma birnin Mombasa na gabar tekun kasar, yayin da aka shafe kwanaki uku ana zanga-zangar tsadar rayuwa a fadin kasar.

 

Zanga-zangar da aka yi a makon da ya gabata ta yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 14.

 

“Gwamnati ta samu sahihin bayanan sirri na tsaro cewa masu aikata laifukan da ke shirin kaddamar da ta’addanci da tashe-tashen hankula a kan jama’a na da niyyar yin artabu da jami’an tsaro a kusa da wasu makarantu a kananan hukumomin Nairobi da Mombasa,” in ji ma’aikatar cikin gida.

 

Rahoton ya ce shugaban ‘yan sanda Japheth Koome ya bayyana zanga-zangar adawa da karin haraji a matsayin haramtacciya, duk da cewa babbar kotun kasar ta yi watsi da bukatar da aka yi mata na ayyana ta a matsayin haramtacce a ranar Litinin.

 

A wata zanga-zangar makamanciyarta a ranar Larabar da ta gabata, ‘yan sanda sun harbe akalla mutane 10.

 

A halin da ake ciki, sama da yara ‘yan makaranta 50 ne kuma aka harba barkonon tsohuwa a lokacin da suke ajin su a birnin Nairobi, inda daga bisani aka garzaya da su asibiti a sume.

 

An samu rahotannin ‘yan sanda sun harba barkonon tsohuwa kan masu zanga-zanga a unguwannin da ke kusa da birnin Nairobi.

 

Yayin da masu zanga-zangar dauke da danyen muggan makamai kuma suka tare tituna a yammacin Kenya tare da karbar kudade daga masu amfani da hanyar.

 

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun yi kakkausar suka ga ‘yan sanda kan abin da suka kira amfani da karfi fiye da kima.

 

Kungiyoyin na cikin gida da na kasa da kasa da jami’an diflomasiyyar kasashen ketare sun bayyana matukar damuwarsu kan halin da ake ciki a kasar Kenya, inda suka bukaci a yi tattaunawa domin tinkarar matsalolin da ake fuskanta.

 

 

BBC/L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *