Take a fresh look at your lifestyle.

Wata Motar Fasinja Ta Kama Da Wuta A Aljeriya

0 129

Jami’an Aljeriya sun ce akalla mutane 34 ne suka mutu sakamakon wani hatsarin mota da ya afku a lardin Tamanrasset da ke kudancin kasar.

 

Hukumar kare hakkin jama’a ta ce wata motar bas ta fasinja ta yi karo da wata motar amfani kafin ta fashe da wuta.

 

Rahoton ya ce an kuma jikkata wasu mutane 12 kuma ba a gano wadanda ke da hannu a lamarin ba.

 

Tamanrasset dai na kusa ne da Nijar da Mali kuma wuri ne da ake yawan tsallakawa bakin haure daga yankin Saharar Afirka da ke kokarin shiga Turai.

 

 

BBC/L.N

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *