Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Taya Musulmi Murnar Sabuwar Shekarar Musulunci

0 88

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya taya al’ummar Musulmin Najeriya da ma duniya baki daya murnar ganin sabuwar shekarar Musulunci ta 1445 Hijira.

 

Ya yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su yi koyi da dabi’un hakuri da juriya da rikon amana kamar yadda Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ya koyar.

 

Ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan kasa da su jure wa kalubalen da ake fuskanta, su kuma kasance da bege tare da tabbatar da cewa kowa ya tashi tsaye wajen cika alkawuran da aka dauka.

 

Shugaban ya yi addu’ar Allah ya sa shekarar Hijira mai zuwa ta kara zaman lafiya da wadata.

https://twitter.com/officialABAT/status/1681621501454286848?ref_src=twsrc%5Etfw%7Ctwcamp%5Etweetembed%7Ctwterm%5E1681621501454286848%7Ctwgr%5E882f15094989a0d155ec8ffc1f45dd0bc00e73c9%7Ctwcon%5Es1_&ref_url=https%3A%2F%2Fvon.gov.ng%2Fpresident-tinubu-congratulates-muslims-on-islamic-new-year%2F

 

L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *