Take a fresh look at your lifestyle.

Tattalin Arziki: Shugaba Tinubu ya ci gaba da tuntubar Masana

0 112

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ci gaba da tuntubar manyan ‘yan wasa kan yadda za a samu tattalin arzikin Najeriya a kan turba mai inganci.

 

Dangane da haka, shugaban kasa da mataimakinsa Kashim Shettima a yammacin Laraba ya gana da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da wasu gwamnonin jihohi da suka hada da na Imo, Kwara, Legas da Ogun.

 

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake, wanda ya bayyana hakan ya ce taron ya kuma duba yadda za’a kammala shirye-shiryen raba kayan agajin domin dakile illar cire tallafin man fetur.

 

A baya dai fadar shugaban kasar ta ba da shawarar raba hatsi da takin zamani ga manoma a wani mataki na inganta samar da abinci a kasar.

 

 

L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *