Take a fresh look at your lifestyle.

Ana Zargin Tunisiya Da Mummunan Cin Zarafi Akan Bakaken Fata A Afirka

0 105

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa Human Rights Watch, HRW ta zargi jami’an tsaron Tunisia da aikata “mummunan cin zarafi” kan bakin haure bakar fata na Afirka da ke yunkurin shiga Turai.

 

Kungiyar yakin neman zaben ta ce ta yi hira da bakin haure da masu neman mafaka sama da 20 tun a watan Maris.

 

Bakwai na daga cikin baki ‘yan Afirka fiye da 1,000 da hukumomin Tunisiya suka kora ko tilasta musu yin jigilar su zuwa yankunan hamadar kasar da Libya da Aljeriya a wannan watan.

 

A halin da ake ciki, shugaba Kais Saied ya zargi bakin hauren da tashe-tashen hankula da kuma sauya fasalin al’ummar kasar.

 

HRW na son Tarayyar Turai ta hana kudaden da za a yi amfani da su wajen mayar da bakin hauren gida.

 

 

BBC/L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *