Take a fresh look at your lifestyle.

MAAN Ta Jaddada Kudurinta Na Tallafama Shirin Gwamnati Na Bunkasa Bangaren Noma A Najeriya

Kamilu LawaL,Katsina.

0 267

Kungiyar manoman masara da sarrafata ta kasa (MAAN) ta jaddada kudurinta na bada gudummuwar ta ga shirin gwamnatin tarayya na bunkasa harkokin noma a najeriya.

 

Shugaban kungiyar na kasa Dr. Bello Abubakar Annoor shine ya bayyana hakan a wajen bikin kaddamar da noman masara na bana a birnin Katsina.

 

Dr. Abubakar Annoor ya bayyana cewa kungiyar manoman masara ta kasa ta sha  alwashin cigaba da hada hannu da kanfanoni masu zaman kansu domin tallafawa manoma musamman yayan kungiyar wajen bunkasa noman masara da aikin gona a fadin najeriya

 

“Muna da kanfanoni masu samar da kayayyakin aikin gona da muke hudda dasu kuma zamu ci gaba da hadin gwiwa da su domin samawa manoman mu kayan aiki.

“Makasudin taruwar mu a yau shine, kaddamar da bada   bashin kayayyakin ba tare da shigowar gwamnati ko bankin yan kasuwa ba domin dogaro da kanmu kamar yadda gwamnati ta koyar damu lokacin da babban bankin CBN ya rika tallafa mamu, daga baya mu ka rika biyan bashin da muka rika karba daga gareshi,” inji Bello Annoor.

 

“yanzu mun hada gwiwa da kanfanoni masu zaman kansu dake samar da kayan aikin gona, mun kaddamar da rabon kayan aikin gona irin su, takin zamani da iraruwa da maganin feshi na ciyawa da na kwari da sauran sinadarai na aikin gonar, da sauran abinda ya shafi injinan aikin gona, kamar su taraktoci da sauran su,”inji shi

 

Ya kara da cewa kaddamar da shirin  noman masarar wanda ya gudana a jihar Katsina na da nufin fadakar da jama’a dake fadin najeriya cewa, dogaro da kai a bangaren noma abu ne mai yiyuwa ba tare da sa hannun  gwamnati ba, kasancewar noma sana’a ce a fadin duniya kuma a najeriya ma za’a iya cimma wannan manufa da nufin bunkasa tattalin arziki da dogaro da kai hadi da samar da guraben aikin yi da cigaban masana’antu a fadin kasa.

 

 

Yace” a daminar bana kungiyar tana sa ran samar da tan miliyan daya da dubu dari takwas da tamanin da biyu na masara, a hecta dubu dari hudu da hamsin da takwas a wuraren noman masarar a fadin kasar nan.

 

 

Shugaban kungiyar manoman masarar wanda ya bayyana jin dadin sa a kan shirin shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu na tallafawa manoma domin samar da wadataccen abinci ga yan kasa, ya kuma yi fatan shugaban zai cika alkawullan da ya daukarwar manoman masara a lokacin yakin neman zabe.

 

 

Kazalika yayi fatan gwamnan jihar Katsina zai saka kwarewar da ya samu a fannin inganta aikin gona domin bunkasa bangaren, domin cigaban al’ummar jihar Katsina da kasa baki daya

Bikin kaddamar da noman masarar na bana ya samu halartar kanfanonin samar da kayan aikin gona daga sassa da bangarorin najeriya

 

 

Kazalika a bikin na bana an kaddamar da bada kayayyakin wanda mataimakin gwamnan jihar Katsina Malam Farouk Lawal Jobe ya jagoranta.

 

Kamilu Lawal,Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *