Take a fresh look at your lifestyle.

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga A Jihar Zamfara Da Sakwato

0 148

Dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan bindiga a kauyukan Mutuwa, Guda Tudu, Kawar, Dantayawa, Gidan Kare, Mahuta, da Gyado na jihohin Zamfara da Sakwato.

 

Wani jami’in leken asiri na tsaro ya shaidawa PRNigeria cewa hadin gwiwar aikin share fage da sojojin suka yi ya kai ga lalata sansanonin ‘yan bindiga a kauyukan.

 

“Hakazalika, sojoji a Forward Operating Base (FOB) Faru da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara da ke aiki da sahihan bayanan sirri, sun kai farmaki a kauyen Bagabuzu.

 

“An kashe ‘yan bindiga hudu yayin da wasu suka tsere da raunukan bindiga.”

PRNigeria ta ruwaito cewa Sojojin sun samu bindiga mai sarrafa kanta,General Purpose Machine Gun (GPMG), FN Rifle, da harsasai na musamman guda 123

 

A halin da ake ciki, Babban Kwamandan Runduna ta 8 Sokoto kuma Kwamandan Rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma Operation Hadarin Daji, Manjo Janar Godwin Mutkut ya yabawa sojojin bisa juriya da jajircewa da kuma samar da ayyukan soji.

 

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su tallafa wa sojojin da sahihan bayanai game da ayyukan ‘yan bindiga domin mayar da martani kan lokaci.

 

 

 

PRNigeria/L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *