Dakarun Soji na ci gaba da kuma bin sahun mayakan IPOB da suka tsere sun kama wani mayakin da suka samu raunuka tare da kwato wasu karin kayayyaki da dama daga hannun masu laifin.
Dakarun Brigade 63 dake aiki karkashin runduna ta 6 ta sojojin Najeriya a safiyar ranar Asabar 22 ga watan Yulin 2023 sun lalata wani yanki na kungiyar IPOB/ ESN a wani dajin da ke Asaba jihar Delta.
Sanarwar da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ya lissafa wasu daga cikin abubuwan da sojojin suka kara kwato.
Wasu daga cikin kayayyakin da aka kwato sun hada da Babura hudu, Bindigogin igwa guda hudu, AK 47 guda biyar, harsashi na musamman guda 18 na 7.62mm, Wayoyin hannu guda 6, Power Bank guda biyu, Gidan Radiyon Sadarwa na Boafeng guda shida da Caja, wayar Android, Laptop guda daya, Tutocin IPOB 13, Injin Janareto guda daya, Gas guda biyar, Gas Uniformed guda biyar. Sauran abubuwa sune katunan ATM guda biyu da agogon hannu.
L.N
Leave a Reply