Jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Anambra sun cafke wasu ‘yan kungiyar asiri guda uku da ke kai hari kan tirelolin Dangote da ke bin manyan tituna a jihar.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu ya fitar, rundunar ‘yan sandan da ke aikin gano bakin zaren ta kai farmaki maboyar ‘yan kungiyar da ke Nnokwa a jihar, inda aka kama wasu mutane uku da suka lalata tireloli biyu.
An gano shugaban daya daga cikin tirelolin da aka lalata yayin da har yanzu ba a gano inda dayar take ba.
An kai wadanda ake zargin ne zuwa gidan yari domin yi musu tambayoyi yayin da kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Aderemi Adeoye, ya umurci hukumar CID ta jihar da ke Awka da ta dauki nauyin shari’ar domin gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da duk wanda ake tuhuma da aikata laifin.
Leave a Reply