Take a fresh look at your lifestyle.

Harin Yan Bindiga: Gwamnan Jihar Neja ya Jajantawa Al’ummar Kagara

Nura Muhammad, Minna, Niger State

0 148

Gwamnan jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya Umar Mohammed Bago ya jajintawa alumma da masarautar kagara dake karamar hukumar Rafi a jihar bisa harin yan bindiga da suka kai a Garin Gabas a yankin Masarautar.

Gwamna Umar Mohammed Bago a cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun Mai magana da yawun sa Bologi Ibrahim ya ce harin abun takaici ne.

Da yake jajantawa alummar, Gwamnan ya kuma bukaci su da su kara hakuri da gwamnati ganin cewar yana fadi tashi don kawo karshen matsalar tsaro dake addabar jihar, kana zai kawowa Yan jihar mafita don tsaron rayuka da dukiyoyin su.

Har ila yau gwamna Umar Mohammed Bago ya bukaci alummar da su kara sanya Ido ga duk wasu shige da fecen da basu gane ba, kana su sanarwa da jami’an tsaro don daukan matakin da ya dace .

Gwamnan ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa yadda suke fadi tashin ganin an kawo karshen matsalar, inda ya ce gwamnatin jihar zata cigaba da basu goyan baya domin samarwa da alummar saukin matsalar dake damun su.

Gwamna Umar Bogo ya kuma yi addu’oin samun sauki ga jami’an tsaron da suka sami rauni yayin bata kashi tsakanin su da maharan, da kuma samu kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su cikin kushin lafiya.

Jami’an tsaron da aka jibge a makarantar furamari na Garin Gabas sun yi dauki ba dadi da yan bindigar a lokacin da suke wucewa da garken dabbobi da ake zaton na sata ne, inda daga nan ne suka budewa jami’an tsaro wuta har suka raunata biyu daga cikin su.

Yanzun haka Jami’an tsaron da suka sami rauni na samun kulawa a cibiyar lafiya ta gwamnatin jihar Neja dake yankin, yayin da Kuma maharan suka yi garkuwa da mutun uku a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *