Take a fresh look at your lifestyle.

Atiku ya roki kotu da ta yi adalci da bukatar shi

0 106

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Alhaji Abubakar Atiku ya roki kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta PEPC da ta yi kira ga jajircewa wajen yin adalci kan karar da ya shigar ta neman soke zaben shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.

 

 

Atiku ya yi nuni da cewa, sabanin barazanar Tinubu, sammai ba za su fado ba a lokacin da kotun koli ta kore shi (Tinubu) a matsayin shugaban Najeriya saboda yawan magudin zabe da ya kai shi ofis.

 

 

A jawabinsa na karshe a rubuce ga kotun, Atiku ya yi watsi da barazanar Tinubu a matsayin wani fanko da aka tura domin tsoratar da Kotun daga tabbatar da adalci a karar da ke kalubalantar zaben Tinubu.

 

 

Atiku ta bakin babban lauyansa, Cif Chris Uche, SAN, ya tuno da jajircewar da kotun koli ta yi a shari’ar Rotimi Amaechi, inda kotun kolin ta ce sam ba za ta fadi ba idan aka yi adalci kamar yadda doka ta tanada.

 

 

Mai shari’a George Adesola Oguntade, wanda ya yanke hukuncin kotun kolin a hukumar, ya ce, “Dole ne in yi adalci ko da sama ta fadi. Gaskiyar ita ce, idan aka yi Adalci, sammai za su zauna a wuri guda kuma a cikin aminci.”

 

 

Baya ga haka, Atiku ya zargi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da yin amfani da sakamakon zaben shugaban kasa domin bai wa Tinubu goyon baya, sannan ya ayyana shi (Tinubu) a matsayin wanda ya lashe zaben ba bisa ka’ida ba.

 

 

Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya yi nuni da yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi kaurin suna wajen murde muradun masu kada kuri’a, inda ya bukaci Tinubu ya yi watsi da shelanta hukumar zabe a ajiye shi kuma a madadinsa, a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben bayan ya samu rinjayen kuri’u na halal.

 

 

L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *