Majalisar dokokin jihar Adamawa ta amince da kudi naira miliyan 974,670 domin siyan taki da masara.
Amincewar dai na da nufin rage wahalhalun da ‘yan kasar ke fuskanta bayan cire tallafin man fetur.
Kayayyakin da za a siyo sun hada da metric ton 2,100 na masara akan kudi N260,000 akan kowace metric tonne da ya kai N546m da metric tonne 900 na taki akan N23,815.00 kan ko wace buhu wanda ya kai Naira miliyan 428,670.
Amincewar ta biyo bayan nazarin wata wasika da gwamnan jihar Ahmadu Fintiri ya aikewa majalisar.
Tun da farko Gwamna Fintiri ya sanar da majalisar cewa gwamnatin jihar na karbar masara da taki a karkashin sanarwar da shugaban kasa ya bayar na samar da abinci a ma’aikatar kudi ta tarayya.
Ya bukaci a amince da a ba ma’aikatar kudi ta tarayya takardar ba da izinin biya (IPSO) a kan kudi Naira miliyan 974,670.
A cewarsa, za a cire kudaden ne daga tushe daga cikin kason da jihar ke bayarwa na wata-wata na tsawon watanni 12.
Shugabar majalisar, Bathiya Wesley, wacce ta jagoranci zaman, ta umurci magatakardar da ya mika kudurin majalisar ga bangaren zartarwa domin daukar matakin da ya dace.
L.N
Leave a Reply