Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Jihar Gombe Ya Nada Sabbin Sakatarorin Dindindin 12

0 223

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin guda 12 a ma’aikatan gwamnatin jihar.

 

Mukaddashin shugaban ma’aikatan, Alhaji Ahmed Abdullahi, wanda ya mika takardar amincewar Gwamnan, ya ce nadin ya samo asali ne a bisa dacewarsu ta fuskar kwarewa, gogewa, kwazon aiki, jajircewa, da amana gami da kwazonsu a jarabawar karin girma da hirarraki. .

 

A cewar mukaddashin shugaban ma’aikatan gwamnati, “nadin ya kuma yi daidai da kudurin gwamnati mai ci na kara karfafa ma’aikatan gwamnati da kuma kudurin tabbatar da cewa ma’aikatan da ke aiki tukuru sun kai kololuwar aikinsu kafin su yi ritaya.”

 

Sabbin sakatarorin din din din sun hada da Mohammed Ibrahim Jalo da Adamu Mohammed Kala daga karamar hukumar Akko; Dr. Ibrahim Yakubu – Balanga; Sa’adatu Bome Ishaya -Billiri; Abubakar Adamu- Dukku, Abdmulkadir Adamu, Abubakar Babayo Hassan, Gombe and Ahmed Mohammed Yunusa – Gombe LGA.

 

Sauran su ne: Mohammed Dantata Ndus – Kaltungo; Abubakar Bella M/ sidi – Kwami; Shuaibu Ibrahim -Shongom da Mohammed Ismail Hina -Yamaltu Deba LGA.

 

Dukkan mukaman Zasu Fara aiki nan take.

 

L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *