Gwamnatin jihar Katsina ta bada kwangilar gina makarantun sakandire 75 a jihar
Kamilu Lawal,Katsina.
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya amince da a fitar da sama da naira miliyan dubu biyu da miliyan dari bakwai domin aikin gina makarantun sakandare 75 a kananan hukumomi 34 da jihar take da su
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Ibrahim Kaula Muhammad, tace bada kwangilar aiyukan na daga cikin kokarin gwamnan na cika alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe
“Gina makarantun ya samu tallafin shirin bankin duniya na AGILE domin bunkasa ilmin sakandiren yaya mata a jihar,” sanarwar ta bayyana
Ta kuma bayyana cewa makarantun da za a gina, sun hada da kanana da manyan makarantun sakandare a dukkanin kananan hukumomin jihar domin ‘ya’yan talakawa su samu ilmi mai inganci kamar yadda gwamnatin tayi alkawali
Sanarwar tace jimillar kudin da za’a fitar domin gudanar da aiyukan wanda kaso ashirin ne na kudin kwangilar sun kai naira miliyan dubu biyu da miliyan dari bakwai da talatin da bakwai da naira dubu dari shidda da ukku (#2,737,603,000)
Gwamnan ya umurci ‘yan kwangilar da su gudanar da aiki mai nagarta kuma su kammala cikin lokacin da aka kayyade masu.
Kamilu Lawal.
Leave a Reply