Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na dijital na Najeriya Farfesa Isa Pantami ya ce gudanar da aiki mai inganci shine mabudin ci gaban harkar sadarwa ta Najeriya a zamanin juyin juya halin masana’antu na hudu (FIR). Pantami ya bayyana hakan ne a taron horar da hukumar kula da harkokin sadarwa ta Najeriya (NCC) a Abuja babban birnin Najeriya. Horon wanda Farfesa Pantami ya jagoranta yana da taken: “Gudanar da Inganci a juyin juya halin masana’antu na 4.”
Leave a Reply