Wata gidauniyar tallafawa cigaban musulunci mai suna “Majalisin juma’a and ta’awanu Islamic foundation” a jihar Katsina dake arewa maso yammacin najeriya ta kaddamar da wani asusu na musamman domin tattara gudummuwar kudade da nufin gina gidaje 400 domin marayu da sauran mabukata a jihar
Cibiyar zata gina gidaje 400 da makaranta da asibiti da wurin koyon sana’o’i da sauran gine gine domin inganta rayuwar marayu da mabukata hadi da yan gudun hijira da matsalar tsaro ta rabo da gidajen su
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin zakka da wakafi na gidauniyar Usman Bn Affan, Sheikh Dr. Ahmad Musa ya bayyana cewa kaddamarwar na da nufin sanar da al’ummar musulmi akan bude asusun da gidauniyar tayi domin su bada gudummuwar su tare da bayyana bukatar da ake da ita akan kowane dayan su ya saka jarinsa domin inganta rayuwar marayun da sauran duk wadanda suke da bukatar tallafin al’umma
Ya bukaci wadanda suka halarci taron su isar da sakon gidauniyar zuwa ga wadanda basu halarta ba domin su ma su saka gudummuwar su da nufin tallafama shirin ya cimma kudurin sa
Dr. Suleiman ya bayyana cewa gina gidaje 400 domin marayu da makaranta da asibiti da cibiyar koyon sana’o’i na daga cikin ayyukan da za’ samar da kudaden da za’a tattara
Yace” kira na ga jama’a su amsa wannan kira, su bada naira dubu daya daya kowanen su, naira dubu dubu muke bukata daga mutum miliyan daya.
“Idan kowanen mu, cikin mutum miliyan daya ya bada naira dubu daya kadai, to zamu samu naira biliyan guda,”
Ya kara da cewa“idan aka samu kudin, kaso sittin nasu zai iya kammala mana ginin gidajen guda 400, yayin da sauran kudaden zasu kammala aikin makaranta da asibiti da wuraren koyon sana’o’in
Yana mai bayyana cewa “masallaci da ofishin gidauniya gasu nan mun gina,”
Da yake jawabi a wajen taron, gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya sanar da bada gudummuwar gwamnatin jihar ta naira miliyan dari daya
Kamar yadda ya bayyana gudummuwar wadda ta kunshi har da ta kananan hukumomin jihar talatin da Hudu (34) na a matsayin kaso goma na gudummuwar da ake kudurin tarawa domin kammala aikin da aka shirya gudanarwa
Gwamnan ya kuma jaddada kudurin gwamnatin jihar na hada hannu da kungiyoyi irin su domin inganta rayuwar marasa karfi da sauran mabukata a fadin jihar
Abubuwan da suka gudana a wajen taron sun hada kaddamar da asusun da karbar gudummuwa daga mutane da dama hadi da dora harsashen gina gidajen a harabar cibiyar
Kazalika, an kaddamar da dashen itatuwan dabino da sauran itatuwan marmari a gonar marayun dake kusa da ginin cibiyar, a garin Dandagoro na karamar hukumar Batagarawa a jihar ta Katsina.
Kamilu Lawal.
Leave a Reply